ABNA24 : Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa kafin sanarwan ta Boko Haram rundunar sojojin na sama ta bada sanarwan becewar jirgin yakinta guda daya, dauke da matuka biyu, a yayin wata fafatawa da mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.
Rundunar ta kara da cewa hotunan da boko haram ta watsa a kafafen sadarwa ta yanar gizo, na burbushin jirgin saman yakin da suka kakkabo ba gaskiya bane, duk da cewa har yanzun basu san inda jirgen da matukansa biyu suka ba.
342/