ABNA24 : A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta buga a shafinta na Facebook ta ce bayan shafe kwanakin killace kai da kuma sake gudanar da binciken likitanci a kan shugaba Asad da maiɗakin nasa ya tabbata cewa sun warke daga cutar ta Coronavirus.
Sanarwar ta ƙara da cewa a saboda haka daga yau Talata, shugaban da maiɗakin nasa za su koma bakin aikinsu ba tare da wata damuwa ba.
A ranar 8 ga wannan wata na Maris ne fadar shugaban ƙasar Siriya ta sanar da cewa shugaba Asad da maiɗakinsa Asma’ sun kamu da cutar ta coronavirus, amma dai babu wata damuwa tattare da su, kawai dai sun killace kansu sannan kuma ana ci gaba da duba lafiyarsu.
342/