ABNA24 : Ita dai ƙungiyar ta SPLM-N da ke ƙarƙashin jagorancin Abdelaziz Al-Hilu ɗaya ne daga cikini ƙungiyoyin ‘yan tawaye guda biyu da suka ƙi sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan wacce take mulki a Sudan ɗin bayan hamɓare gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Umar Hasan al-Bashir a shekara ta 2019.
Wannan yarjejeniyar da aka cimma a birnin Juba, babban birnin ƙasar Sudan ta Kudu a jiya Lahadi ta shata wasu batutuwa da za a ba su muhimmanci da suka haɗa da haɗe sojoji da kuma kafa gwamnati irin ta demokraɗiyya wacce ba ruwanta da wani addini wacce kuma za ta ba wa kowa ‘yancin yin addinin da ya ke so.
Haka nan kuma yarjejeniya ta tabbatar da cewa amfani da ƙarfin soji ba zai tabbatar wa ƙasar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba don haka tattaunawa da bin tafarki na siyasa ita ce mafita.
Cimma wannan yarjejeniyar dai yana nufin yanzu za a fara tattaunawa tsakanin gwamnatin Sudan ɗin da ƙungiyar ta SPLM-N wacce take riƙe da wani ɓāngare mai yawa na lardunan Blue Nile da kuma Kudancin Kordofan na ƙasar ta Sudan.
342/