29 Maris 2021 - 19:41
Masar:An Cire Kataparen Jirgin Ruwan Daukar Kaya 'Ever Given' Wanda Ya Makale A Mashigar Ruwa Ta Suez Daga Inda Ya Makale A Yau

Tun ranar tarlatan da ta gabace wani kataparen jirgin ruwan daukar kaya mai suna ‘Ever Given’ya Makale a mashigar ruwa ta Suez ta kasar Masar sanadiyyar iska mai karfi da ta kora shi zuwa inda ya makale. Makalewar dai ya yi sanadiyyar hana sauran jiragen ruwa wucewa ta mashigar.

ABNA24 : ‘Ever Gigen’ mai tsawon mita 400 yana daga cikin jiragen ruwa mafi girma a duniya, makalewarsa a wannan mashigar dai ya jawo asorori namiliyoyin dalar Amur ga kasar ta Masar sannan ya sanya wasu jiragen ruwa sauya hanya.

Labaran da suke fitowa dag kasar Masar sun nuna cewa a safiyar yau litin aka sami nasarar cire jirgin daga inda ya makale, kuma ana saran nan da yan sa’o’i dimbin jiragen ruwa da suke jiran wucewa ta mashigar zasu fara wucewa.

An kiyasta cewa gwamnatin kasar masar tana samun dalar Amurka kimani miliyon 400 a kowa ce sa’a ta mashigar ruwan. Mashigar ruwa ta Suez dai na daga cikin mafi muhimmancin irinta a duniya, don yadda ta takaita tazarar safara daga yankin Asia zuwa kasashen yamma.

342/