ABNA24 : Zanga zangar dai na zuwa ne, kwana guda bayan mutuwar wasu mutane shida sakamakon wani harin sojojin Faransar.
Rundunar sojin Faransa ta ce ta kai harin ne kan masu fafutukar jihadi a arewa maso gabashin Malin, amma mazauna yankin sun ce matasa ne da ke farauta aka kashe.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake gudanar da zanga zangar kin jinin sojojin Faransa a kasar ta Mali dake yankin Sahel inda Faransar ta jibge dakaru 5,100.
342/