ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya nakalto shugaban ya na fadar haka ne a wani jawabin da ya gabatar wa jami’an kiwon lafiyar ta kafar Badiyo a nan birnin Tehran.
Rouhani ya kara da cewa a halin yanzu watannin 13 kenan wadannan jami’an kiwon lafiya suke fafatawa da cutar ta korona a kasar, kuma kokarinsu ne ya sa har yanzun adadin wadanda suke rasuwa a ko wace rana a duk fadin kasar ya tsaya kasa da 100.
Daga karshe shugaban ya bayyana fatansa na ganin an kawo karshen cutar a wannan sabuwar shekara ta 1400 da muka shiga.
Jami’an kiwon lafiya kimani 300 suka rasa rayukansu tun farkon bullar cutar a shekarar da ta gabata a duk fadin kasar.
342/