22 Maris 2021 - 08:19
Shugaban Kasar Iran Ya Ce Shekara Ta 1400 Shekara Ce Ta Kawo Karshen Wahala Da Kuma Samun Bunkasar Tattalin Arziki

Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rouhani ya bayyana cewa babu wata tamtama shekara ta 1400 shekara ce ta sake farfadowar bunkasar tattalin arzikin kasar Iran da kuma cimma sakamako mai kyau na turjiyar da kasar ta yin a tsawon shekaru 3 ga takunkuman tattalin arziki mafi muni wanda Amurka ta dorawa kasar.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaranb Iran Press ya nakalto shugaban yana fadar haka a safiyar yau Lahadi daya ga watan Farvardin na shekara ta 1400, a taron majalisar tattalin arziki ta kasa a nan Tehran.

Shugaban ya kara da cewa gagarumin aikin da gwamnatin kasar ta yin a shekaru 3 da suka gabata, wadanda suka kasance cikin takunkuman tattalin arziki mafi muni wadanda Amurka ta dorawa kasar, a wannan shekarar da kuma shekaru masu zuwa za’a fara ganin amfanin ayyukanta.

Har’ila yau a taron ne shugaban ya bawa ministan tattalin arzikin kasar ya gaggauta samar da tsari wacce zata taimakawa gwamnati wajen gano matsalolin da suke hana ci gaban tattalin arzikin kasar Iran a wasu bangaroriri, don fara aiki a warwaresu.

Daga karshe shugaban ya bukaci hadin kan bangarorin gwamnati guda uku don ganin an kawo ci gaba mai dorawa a dukkan bangarorin kasar.

342/