13 Maris 2021 - 13:55
Najeriya:’Yan Bindiga Sun Sace Yan Makaranta A Jihar Kaduna Na Arewacin Kasar

Majiyar ‘yansanda a birnin Kaduna na tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun sace wasu yan makaran a jiya Alhamis da yamma.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto wani mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar da kuma gwamnatin jihar ta Kaduna suna tabbatar da labarin a safiyar yau Jumma’a.

Muhammad Jalige kakakin ‘yansanda a jihar ya bayyana cewa dailiban da aka sace ‘yan wata makaranta ce ta koyon aikin raya Hamada, sannan ya kara da cewa har yanzun basu tabbatar da adadin daliban da aka sace ba.

342/