ABNA24 : Gwamnatin Jihar Kaduna dai tana ta jan kafa a shari’ar da akewa shehin malamin ba tare da wani dalili na jinkirta ta ba.
Tun cikin watan Disamban shekara ta 2015 ne sojoji suka farwa gidan Shehin Malamin da ke Zariya inda suka kashe mutanen da dama daga ciki har da mata da yara.
Har’ila yau a ranar Laraba da Alhamis 18-19/11/2020 ne Lauyoyin gwamnatin jihar Kaduna suka fara gabatar da shedunsu na tuhume-tuhme da suke wa Sheikh Zakzaky da matarsa. Ana saran a zaman yau da gobe ma zasu ci gaba da gabatar da shaidun ne.
Kotun ta tarayya ta bukaci a saki Sheikh Zakzaky tare da maidakinsa da kuma biyansu diyya kan asarorin da aka jawo musu, amma har yanzu ba a aiwatar da umarnin na kotu.
342/