ABNA24 : Jami’an tsaro na kasar ta Iraki, na sama da na kasa kimani 10,000 ne aka ware don tabbatar da tsaro a ziyarar tarihi wanda Paparoman ya ke yi a kasar ta Iraki.
A yau dai Paparoman ya gana da Ayatullahi Sistani sannan ya je garin Ur na annabi Ibrahim (a) inda ya gana da mabiya addinai daban-daban.
Sai kuma gobe Lahadi ana saran Paparoman zai je Arbil na yankin Kurdistan na kasar ta Iraki, sannan zai kammala ziyarar a ranar Litinin bayan ziyarar wasu coci-coci a birnin Musil wacce ‘yan ta’adda suka tama mamayewa.
Ofishin Ayatullahi Ali Sistani ta bayyana a shafinta na yanar gizo bayan ganawarsa da Paparoman, kan cewa kiristoci a kasar Iraki za su ci gaba da rayuwa da sauran mutanen kasar kamar yadda sauran ‘yan kasar suke rayuwa.
342/
