6 Maris 2021 - 08:27
Fafaroma Francis, Na Ziyara Irinta Ta Farko A Kasar Iraki

Yau, Juma’a, Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis, zai fara wata ziyara mai cike da tarihi a kasar Iraki.

ABNA24 : Ziyarar, ta kwanaki uku ita ce irinta ta farko ta wani fafaroma a kasar ta Iraki.

An tsara fafaroman zai ziyarci biranen Bagadaza, da Najaf da kuma Ur, a kusancin kasar, sai kuma Erbil, Qaraqosh da Mossoul a arewacin kasar.

An dai karfafa matakan tsaro gabanin ziyarar ta Fafaroman.

342/