4 Maris 2021 - 08:34
Rasha : Babu Shakka Za Mu Mayar Wa Amurka Da Turai Martani_Lavrov

Kasar Rasha, ta ce tana nan tana tunanin matakin maida martani game kan takunkuman da Amurka ta kakaba mata na baya bayan nan.

ABNA24 : Fadar Kremlin, ta sanar cewa wannan siyasar ta takunkumi ba zata hana ta cimma muradunta ba, tare da sha alwashin maida maratani kamar kullun ga Amurkar har ma da kasashen turan.

Rasha, ta ce, babu wani sauyi da za’a samu game da batun Navalny, wanda kasashen yamma suke amfani da shi a yunkurin cimma manufofinsu kan kasar ta Rasha, sabodaBabu wata hujja da suke da ita game da batun amfani da guba kan Navalny.

A shekaran jiya ne, Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu hukumomin Rasha da wasu ‘yan kasar, bisa zarginsu da hannu wajen sanyawa Alexei Navalny guba.

Da yake yiwa manema labarai karin haske kan lamarin, wani babban jami’i a gwamnatin Amurka ya bayyana cewa, hukumomin leken asirin Amurka sun gano cewa, hukumar leken asirin tarayyar Rasha, ta sanyawa dan adawa Navalny gubar nan ta Vovichok, a ranar 20 ga watan Agustan shekarar 2020.

Jami’in ya kara da cewa, wannan shi ne mataki na farko da Amurka ta dauka kan wannan batu, kuma wasu kari na nan tafe. Yana mai cewa, Amurka za ta yi aiki tare da kawayenta na Turai, wajen yin kira da a tunkari Rasha.

342/