2 Maris 2021 - 11:07
Rauhani: Iran Ta Kusa Daina Dogaro Da Man Fetur Domin Samun Kudin Shiga

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya ce Iran tana da tsarin da take aiki da shi wanda zai kawo karshen dogaron da take yi da man fetur, kuma a yanzu hakan ma ba shi ne take dogaro da shi ba wajen samun kudin shiga.

ABNA24 : Wani sashe na jawabin shugaban kasar ta Iran ya ce; A halin yanzu a kowace shekara Iran tana samun kudin shigar da su ka kai dalar Amruak biliyan 31 daga kayan da take fitarwa wadanda ba su da alaka da man fetur.Bugu da kari, Dr. Hassan Rauhani ya ci gaba da cewa; Saboda rashin dogaro da Iran da man fetur din, Amurka ba ta da mafita illa ta dauke wa Iran takunkumin da ta kakaba ma ta na man fetur.

342/