1 Maris 2021 - 07:24
Hare haren Baya Bayan Nan a Iraki, Akwai Makirci A Ciki_Zarif

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bayyana shakku game da hare haren baya baya nan a Iraki, wadanda a cewarsa akwai makirci a ciki.

ABNA24 : Ababen dake faruwa a Iraki, musamman har eharen baya baya nan wani yunkuri da wasu ke yi na neman tada fitina da kuma dagula alakar dake tsakanin Iran da Iraki.

Haka zalika ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya yi tir da matakin Amurka na kai hari kan dakarun Iraki, wanda ya ce hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa, hasali ma keta hurimin kasar Iraki ne.

Iran, ta bukaci gwamnatin Iraki, data dau matakin gano wadanda ke da hannu a wannan yunkuyin na neman tada hargitsi, da ya ce ana yinsa ne domin haddasa riki tsakanin mahukuntan Bagdaza da Tehran.

A nata bangare Iraki, ta jaddada cewa ba zata yarde wani mahaluki ya lalata alakar dake tsakanin kasashen biyu ba.

342/