ABNA24 : Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana wadannan hare-hare da cewa sun hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa, kuma hakan yana a matsayin keta hurumin kasashen biyu masu cikakken ‘yanci.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, bai kamata wasu kasashe su mayar da kasar Syria ta zama wurin kece raini tsakaninsu da wadanda suke takon saka ba.
Lavrov ya ci gaba da cewa, bayanan da Rasha ta samu suna tabbatar da cewa, sabuwar gwamnatin Amurka ba ta nufin fitar da sojojin kasar daga Syria, amma kuma a yanzu ba gadin rijiyoyin danyen manfetur na Syria za su yi ba, za su yi shirin ci gaba da zama kasar ne har sai abin da hali ya yi.
Ita ma a nata bangaren gwamnatin kasar Syria ta bayyana harin da cewa, hakan babbar manuniya akan cewa sabuwar gwamnatin Amurka ba ta da kyakkyawar manufa dangane da Syria, inda hakan ke kara tabbatar da cewa ita za ta bi sahun gwamnatin da ta gabace ta ne wajen ci gaba da kara ruruta wutar rikici a kasar.
A nata bangaren gwamnatin Iran, ta bayyana cewa harin na Amurka ya kara fito da manufar sabuwar gwamnatin Amurka a fili dangane da abin da yake faruwa a Syria, kuma hakan abin kunya ne da Allawadai.
Gwamnatin kasar Venezuela ma ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da hare-haren na Amurka a Syria, tare da bayyana cewa wannan salon gwamnatin Amurka da ta gabata ce, na keta dokokin kasa da da kasa.
342/