14 Faburairu 2021 - 13:58
Lauya Karim Khan Ya Zama Sabon Mai Shigar Da Kara Na Kotun ICC

An zabi Karim Khan, a matsayin sabon babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya cewa da ICC.

ABNA24 : M. Khan wanda lauya ne dan asalin kasar Biritaniya an zabe shi da kuri’u 72 daga cikin 123 na mambobin kotun a zagaye na biyu na zaben da ya gudana ranar Juma’a.

Kafin zabensa Karim Khan, shi ne ke jagorantar binciken MDD, kan laifufukan kungiyar Da’esh a kasar Iraki.

Sabon mai shigar da kara na kotun zai kama aiki a ranar 15 ga watan Yuni mai zuwa.

Zai kuma maye gurbin Fati Bensouda, ‘yar asalin kasar Gambia, wadda wa’adinta na shekaru tara tana jagorancin kotun zai kawo karshe.

Mme Bensouda ta yi kaurin suna saboda gudanar da bincike kan yakin Afghanistan da rikici tsakanin Israila da Falasdinu.

342/