13 Faburairu 2021 - 11:58
Kotun ICC Na Zaben Wanda Zai Gaji Fatou Bensouda

Kotun Hukunta manyan laifuffuka ta Duniya cewa da ICC, ta fara gudanar da taron ta domin zabar wanda zai maye gurbin Babbar mai shigar da kara ta kotun Fatou Bensouda sakamakon kawo karshen wa’adin aikin ta.

ABNA24 : Yanzu haka 'yan takara 4 dukkan su maza ne ke fafatawa domin maye gurbin Bensouda wadda ta fito daga kasar Gambia.

Mme Bensouda ta yi kaurin suna saboda gudanar da bincike kan yakin Afghanistan da rikici tsakanin Israila da Falasdinu.

Yan takarar sun fito ne daga kasashen Birtaniya da Ireland da Italia da kuma Spain, amma babu guda daga cikin su da ya samu nasara wajen samun kuri’un da ake bukata a kuri’ar da aka kada ta farko.

Amma Karim Khan, lauya ‘dan kasar Birtaniya ne ke sahun gaba.

342/