ABNA24 : Sai dai majiyoyin HKI sun bayyana cewa kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi kokarin kakkabo jirgen saman leken asirin kasar, wanda ake sarrafa shi daga nesa, amma makamin bai same shi ba.
A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ma, kungiyar ta Hizbullah ta kakkabo wani jirgin leken asirin yahudawan a sararin samaniyar kudancin kasar. Har’ila yau an kakkabo irin wannan jirgin a yankin Gazza na kasar Falasdinu da aka mamaye a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
342/