ABNA24 : Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta nakalto Jake Sullivan mai bawa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaro yana fadar haka, a lokacinda yake zantawa da tokwaransa na kasar Afganistan a jiya Asabar.
Sullivan ya kara da cewa, abinda gwamnatin za ta shi ne tabbatar da cewa kungiyar Taliban ta na aiki da yarjejeniyar. A nashi bangaren mai bawa shugaban kasar Afganistan shawara kan harkokin tsaro Hamdullahi Mohib ya ce bukatarsu ita ce tabbatar da zaman lafiya a kasar Afganistan.
A cikin watan Fabrairun shekarar ta da ta gabata ne, Amurka ta kulla yarjejeniya da kungiyar Taliban ta kasar Afganistan, da sharadin Amurka zata fidda sojojinta gaba daya daga kasar a karshen shekara ta 2021.
342/