ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran ƙasar Yemen ya bayyana cewar ministan harkokin wajen ƙasar ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a yau ɗin nan Lahadi inda ya ce matuƙar dai aka hana Yemen zaman lafiya toh kuwa Saudiyya a matsayinta na mai wuce gona da iri, ita ma ba za ta zauna lafiya ba.
Ministan harkokin wajen na Yemen ya ci gaba da cewa: Bai kamata waɗanda suke turo sojojin hayarsu zuwa ƙasar Yemen da nufin yin kisa da lalata garuruwa da ƙauyukanta, su yi tsammanin za mu dinga aika musu da furanni da kuma tattabarun zaman lafiya ba ne.
Minista Abdullah ya kirayi cibiyoyin ƙasa da ƙasa da kuma sauran ƙasashen duniya da kada su bari abubuwan da mahukuntan Saudiyya suke faɗi dangane da dalilansu na kai hari ƙasar Yemen su yaudare su yana mai kiran su da su buɗe idanuwansu su gane wa kawukansu haƙiƙanin abubuwan da suke faruwa a ƙasar.
Kimanin shekaru shida kenan Saudiyya da ƙawayenta suka ƙaddammar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Yemen da sunan dawo da gwamnatin hamɓararren shugaban ƙasar inda ya wuce yanzu dubun dubatan al’ummar ƙasar ne suka rasa rayukansu baya ga dubun dubatan da suka samu raunuka da kuma waɗanda suke cikin hali ƙa-ƙa-ni-ƙa-yi.
342/