ABNA24 : Gwamnatin Donald Trumph mai barin gado ta dawo da takunkumin da tsohon shugaban kasar ta Amurka Barack Obama ya daukewa Iran bisa yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin ta da sauran kasashe masu karfi na duniya. Kuma ya fice daga yarjejeniyar da aka cimma matsaya akai rana tsaka.
A nasa bangaren jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatullah sayyid Ali khamina’I ya bukaci kasar da kada ta bata lokaci koda sa’a daya ne kan batun cire takunkumin makutar hakan zai yi wu ta hanyar da ta dace da za ta bada tabbacin kare mutunci da martabar kasar
Wannan yana zuwa ne bayan da zababben shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana aniyarsa na sake komawa kan yarjejeniyar nukiliyar iran da aka cimma matsaya akai.
342/