ABNA24 : An dai tsaurara matakan har zuwa ranar 15 ga watan Janairu na shekara mai shirin kamawa.
Daga cikin matakan da aka dauka har da haramta shan barasa a bainar jama'a da wuraren shakatawa kamar su bakin ruwa daga ranar Alhamis, a wani yunkuri na rage taruwar jama'a, inji shugaban kasar.
An kuma kafa dokar hana fitar dare daga bakin karfe 10 na dare, a yankunan da ake fuskantar karuwar cutar, sai kuma karfe 12 dare a sauren sassan kasar.
Haka kuma an rage adadin mutanen da za a bari su halarci dakin taro zuwa 100, haka kuma wadanda za su gudanar da taro a fili adadinsu ba zai wuce 250.
A ranar Laraba data gabata dai mutane 4,400 ne aka rawaito cewa sun harbu da cutar ta korona a Afrika ta Kudu, wanda su allaluma mafi girma da aka samu a kasa da sa’o’I 24 tun bayan watan Agusta da ya gabata.
342/