24 Nuwamba 2020 - 12:13
Kasashen Tanzaniya Da Mozambique Sun Fara Wani Shiri Na Fada Da Ta’addanci A Kasashen Su

Kasashen Mozambique da Tanzaniya sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar aiki tare da nufin fada da ‘yan ta’addan da suke da alaka da kungiyar ISIL da suke ci gaba da barazana ga yankunan da suke kan iyakokinsu musamman a lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar Mozambique din.

ABNA24 : Jaridar Noticias mallakin gwamnatin kasar Mozambique ta buga labarin cewa manufar yarjejeniyar wacce aka kulla tsakanin rundunonin ‘yan sandan kasashen biyu ita ce bin hanyoyin da suka sawwaka wajen ganin bayan ‘yan ta’addan da kuma hukumta su.

Jaridar ta jiyo sufeto janar na ‘yan sandan Mozambique din Bernardino Rafael yana fadin cewa daya daga cikin manyan manufar yarjejeniyar ita ce dawo da dukkanin ‘yan ta’addan da ake tsare da su a kasar Tanzaniya gida don a hukunta su, kamar yadda kuma ya ce yarjejeniyar za ta ba wa jami’an tsaron kasashen biyu damar sanya ido kan iyakokin kasar musamman wajejen da ‘yan ta’addan suke gudanar da ayyukansu.

Rikici da ayyukan ta’addanci ya fara bayyana a yanki na Cabo Delgado mai arzikin iskar gas ne a watan Oktoban 2017 lokacin da wasu masu dauke da makami wadanda daga baya suka sanar da mubaya’arsu ga kungiyar ISIL suka kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda a garin bakin ruwan nan na Mocimboa da Praia, tun daga lokacin kuma sama da mutane 2,200 ne aka kashe kana wasu dubbai kuma suka gudu daga yankin sakamakon ci gaba da ayyukan wadannan ‘yan ta’addan a yankin.

A halin yanzu dai ayyukan ‘yan wadannan kungiya yana ci gaba da fadaduwa sakamakon ci gaba da samun goyon bayan wasu mayakan da aka ce suna fitowa ne daga kasar Tanzaniya.

342/