9 Nuwamba 2020 - 12:52
Najeriya: Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda Ya Ba Da Umurnin Janye ‘Yan Sanda Daga Masu Gadin Wasu Manyan Kasar

Babban sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya ba da umurnin janye jami’an ‘yan sandan da aka sanya su cikin masu gadin wasu fitattun mutane a kasar ba tare da bata lokaci ba.

ABNA24 : Rahotanni sun ce umurnin janye jami’an ‘yan sandan yana cikin wani sako ne da sufeto janar din ya aike wa mataimakan sufeto janar din da kuma dukkanin kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin kasar na su fara aiwatar da wannan umurnin.

Manyan jami’an da abin ya shafa dai sun hada da wasu ‘yan majalisa tsoffi da masu ci, tsoffin ministoci, tsohon sakataren gwamnatin tarayya da kuma wasu shahararrun masu kudi da masu fadi a ji.

Daga cikin mutanen da abin ya shafa, kamar yadda kafar watsa labaran nan ta Premiumtimes ta fadi har da wasu ‘yan majalisa masu ci irin su Nicholas Mutu da Shina Peller, sai kuma wasu tsoffin ‘yan majalisa da suka hada da Lado Yakubu da Boroface Ajayi, sai kuma tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal, tsoffin ministocin da abin ya shafa kuwa su ne Femi Fani-Kayode da Bashir Yuguda.

Ana ganin wannan mataki na gaggawa din dai yana cikin shirin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kasar take yi na yin gyaran fuska ga rundunar ‘yan sandar kasar wanda wasu daga cikin ayyukanta suka janyo zanga-zangogin da suka faru a kasar cikin makonnin da suka gabata.

342/