29 Oktoba 2020 - 13:37
​Zaben Amurka: Joe Biden Ya Kada Kuri’arsa A Jihar Delaware

Dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Democrat Joe Biden ya kada kuri’arsa a mahaifarsa jihar Delaware.

ABNA24 : Rahotanni sun ce bayan kada kuri’ar tasa, Joe Biden ya yi dan takaitaccen bayani kan matsalar da kasar take ciki dangane da batun corona, inda ya dora alhakin hakan a kana bin da ya kira gazawa daga gwamnatin Trump.

Joe Biden ya yi alkawarin cewa idan har ya lashe zaben shugaban kasar ta Amurka, to za a samar da allurar rigakafin corona, ta yadda kowa zai same ta kyauta a kasar Amurka.

Yanzu haka dai fiye da mutane miliyan 74 ne suka kada kuri’unsu a zaben na Amurka, wanda aka fara shi da wuri, domin kaucewa cunkoso saboda cutar corona, inda a ranar Talata mai zuwa ne za a gudanar da zaben a hukumance.

Shi ma shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya kada tasa kuri’ar a jihar Florida a ranar Asabar da ta gabata.

342/