ABNA24 : A wata sanarwa da Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta fitar, ta ce bisa la’akari da cewa jakadar kasar Faransa ba ya nan, don haka ma’aikatar ta kirayi mai kula da ofishin jakadancin, Florent Aydalot, inda ya gana da mataimakin babban darakta bangaren lamurran kasashen Turai na ma’aikata.
A yayin wannan ganawar, an sanar da jami’in diplomasiyyar rashin jin dadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan kalaman wasu jami’an gwamnatin Faransan wadanda suka sosa zukatan musulmin duniya. Ma’aikatar wajen ta Iran tace an shaida wa jami’in na Faransa cewa duk wani cin mutumci da kuma zarafin Annabi (s.a.w.a) da kuma koyarwar Musulunci abin yin Allah wadai da shi ne kuma ba za ta taba amincewa da shi ba koda kuwa daga wajen waye.
Cikin ‘yan kwanakin nan dai ana ci gaba da tofin Allah tsine da kuma kakkausar suka ga kalaman wasu jami’an gwamnatin Faransan musamman shugaban kasar Emmanuel Macron wanda ya nuna goyon bayansa da zanen batanci da cin zarafin da aka yi wa Annabi (s.a.w.a) a kasar da kuma bayyana hakan a matsayin ‘yancin fadin albarkacin baki.
342/