ABNA24 : A lokacin da yake gabar da jawabi a yau a gaban majalisar dokokin kasar Iran a birnin Tehran, Shugaba majalisar Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada matsayin gwamnatin kasar Iran, na kin amincewa da duk wani nau’in cin zarafi da tozarci ga manzon tsira (SAW).
Ya ce a cikin ‘yan kwanakin nan kowa ya ga yadda yin batunci ga manzon Allah (SAW) ya zama wani abu na yin Gadara da shi a kasar Faransa, inda kowa ya ga dama zai iya fitowa ya yi batunci da cin zarafi a kan manzon Allah a kasar, bisa hujjar ‘yancin fadar albarkacin baki.
Qalibaf ya ce mutanen da ba su iya jurewa suka komai karancinta, za su ta kumfan baki kamar za su tayar da duniya, amma kuma a lokaci keta alfarmar addini mai mabiya sama da biliyan 1.8 a duniya, hakan ba laifi ba ne a wurinsu.
Dangane da matsayar da gwamnatin kasar Faransa ta dauka na mara baya ga wannan cin mutunci ga addinin muslunci ta hanyar tozarta matsayin ma’aiki mai daraja, ba abu ne da dukkanin al’ummar musulmi za su yi shiru a kansa ba, a kan haka gwamnatin Faransa ta yi hattara kana bin da take yi na neman tunzura musulmi da jawo fushinsu a kanta.
342/