24 Oktoba 2020 - 12:21
Zarif: Amurka Ba Ta Da Shaáwar Ganin An Sami Zaman Lafiya A Duniya

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya rubuta sako a twitter cewa; Amurka ba ta son ganin zaman lafiya ta wanzu a duniya, abinda yake gabata shi ne sayar da makamai.

ABNA24 : Ministan harkokin wajen na Iran ya yi ishara da yadda ba ta son sabunta yarjejeniyar rage gasar kera makamai ta ( SNV-111) wacce daya ce daga cikin yarjejeniyoyi mafi muhimmanci na tabbatar da tsaro a duniya wacce za ta zo karshe a watan Febrairu na 2021.

Ita dai wannan yarjejeniyar ta shafi rage gasar kera makaman Nukiliya a tsakanin Amurka da Rasha. An kulla yarjejeniyar ne dai a karon farko a ranar 10 ga watan Aprilu a 2010,kuma an fara aiki da ita a ranar 5 ga watan Febrairu na 2011, sannan kuma za ta kare a 2021.

342/