14 Oktoba 2020 - 08:09
​Haniyah: Tarihi Ba Zai Taba Mantawa Da Wadanda Suka Ha’inci Palastinu Ba

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falastinu, Hamas, Ismail Haniyah ya sake yin kakkausar suka ga yarjejeniyar sulhun da aka cimma tsakanin Isra’ila da kasashen UAE da Bahrain yana mai cewa ko shakka babu tarihi ba zai taba ‘ambato mai kyau’ ga kasashen larabawan da suke ha’inci al’ummar Palastinu ba.

ABNA24 : Malam Haniya ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da kafar watsa labarai ta Middle East Eye (MEE) inda ya ce kasashen larabawan da suka kulla sulhu da yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila su za su yi hasara a gaban haramtacciyar kasar Israi’ilan kuma ko shakka babu za ta ci gaba da yi musu barazana.

Jami’in kungiyar ta Hamas ya ci gaba da cewa: Sahyoniyanci wani shiri ne na mamaya. Manufarsa ita ce kafa babbar Isra’ila. Don haka ba ma son ganin an yi amfani da Hadaddiyar Daular Larabawa, ko Bahrain ko Sudan wajen cimma wannan manufar. Tabbas tarihi ba zai yi rahama, sannan mutane ba za su taba mantawa da su ba kamar yadda kuma ‘yan adamtaka ba za ta taba gafarta musu ba.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin Amurka ta shiga tsakanin wajen kulla wata yarjejeniya ta sulhu tsakanin Hadaddiyar Daular larabawa da Bahrain da kuma HKI, inda a halin yanzu kuma take ci gaba da kai gwauro ta kai mari wajen ganin ta shigo da kasashen Sudan da Oman cikin wannan yarjejeniyar.

342/