12 Oktoba 2020 - 15:25
Sheikh al-Azhar Yayi Kakkausar Suka Ga Kalaman Shugaban Faransa Kan Musulunci Da Musulmi

Shugaban jami’ar al-Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmad al-Tayyib yayi kakkausar suka ga kalaman shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron inda ya siffanta musulmi da ‘yan ta’adda yana mai cewa wannan kalamin yaudara ce wacce da dama sun yarda da shi hatta ma wasu daga cikin musulman.

ABNA24 : Sheikh al-Azhar din ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce kalmar musulmi ‘yan ta’adda wata yaudara ce kawai wacce hatta wasu daga cikin musulmin sun fada tarkon wannan yaudarar.

Shehin malamin ya ci gaba da cewa: Hakikanin lamarin shi ne cewa musulmi su ne tushen gina duk wani ci gaba a duk inda suke hatta a cikin kasashen Turai. Yana mai cewa a halin yanzu musulmi suna fuskantar wani kokari ne na bata musu suna da kuma auna su da wasu ma’auni na daban.

A kwanakin baya ne dai shugaban kasar Faransan Emmanuel Macron ya bayyana cewar Musulunci yana cikin tsaka mai wuya da kuma mai da shi saniyar ware a duk duniya lamarin da ya fuskanci mai da martani da tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na musulmi.

342/