11 Oktoba 2020 - 13:29
​China: Ba Za Mu Goyi Bayan Takunkumin Amurka A Kan Iran Ba

Gwamnatin kasar China ta jaddada cewa, ba za ta goyi bayan duk wani yunkurin Amurka da ke neman rusa yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran ba.

ABNA24 : Ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi ne ya bayyana hakan a yammacin jiya, a lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, wanda yake gudanar da ziyrar aiki a kasar ta China.

Wang Yi ya ce; Amurka tana yin gaban kanta wajen daukar matakai da suka yi hannun riga da kudirin majalisar dinkin duniya a kan shirin Iran na nukiliya, wanda kuma kasar China ba za ta taba mara wa Amurka baya a kan haka ba.

Ya ci gaba da cewa, matakan da Amurka take dauka da suka hada da ficewa daga cikin yarjejeniyar, da kuma kakaba takunkumai kan Iran, dukkaninsu abubuwa da suka saba wa ka’ida, wanda shi ma China ba za ta lamunta da hakan ba.

Ministocin harkokin wajen kasashen biyu China da Iran, sun tattauna a kan batutuwa da dama, da suka hada da kara bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki a tsakaninsu, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa da kuma yankin gabas ta tsakiya.

342/