7 Oktoba 2020 - 12:55
Isra’ila Ta Rusa Gidagen Falasdinawa 166,000 Tun Bayan Samuwarta

Gwamnatin Harantacciyar kasar Israel ta rusa gidajen Falasdinawa 165,690 tun bayan mamayar da tayiwa kasar Falasdinu a shekara 1948.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto “Cibiyar tattara bayanai na Falasdina” tana fadara haka ta kuma kara da cewa rushe-rushen gidajen ya fi shafi birnin Qudus da kuma yankin yamma da Kogin Jordan.

Labarin ya kara da cewa gwamnatin yahudawan Sahyoniya sukan fake da cewa an gina gidajen ba bisa ka’ida ba wajen rusa su. A birnin Qudus kadai a halin yanzu akwai falasdinawa 25,000 wadanda suke bukatar gidaje da gaggawa saboda an rusa nasu.

Har’ila yau yahudawan sun yi sanadiyyar hijirar Falasdinawa kimani miliyon guda zuwa ciki da kuma wajen Falasdinu saboda an rusa gidajensu.

A shekara ta 2020 kadai yahudawan sun rusa gidajen Falasdinawa 450 sannan wani lokacin suna tilastawa Falasdiwa rusa gidajensu da kansu ko kuma su biya kudin rusa gidajen.

342/