7 Oktoba 2020 - 12:49
​Trump: A Shirye Nake Domin Sake Tafka Muhawara Tare Da Joe Baiden

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, ya samu karfin jikinsa fiye da yadda yake shekaru 20 da suka gabata, bayan da ya shafe kwanaki uku a jere kwance a sibitin, sakamakon kamuwa da cutar corona.

ABNA24 : A cikin bayanin da ya wallafa a shafinsa na twitter, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, a shirye yake domin tafka wata muhawara tare da abokin hamayyarsa Joe Biden, a ranar 15 ga wannan wata na Oktoba a birnin Miami.

Ya ce hakika muhawarar mai girma ce, amma kuma a shirye yake, domin kuwa ya samu karfin jikinsa, kuma yana kira ga jama’a da kada su dauki cutar corona a matsayin wani abin tsoro.

Tun bayan bullar cutar corona a farkon wannan shekara, Donald Trump ya yi ta yin kalamai na izgili da batun, wanda hakan yasa Amurkawa da dama suke ganin cewa, sakacin da ya yi da batun ne yasa cutar ta yi kamari a Amurka fiye da ko’ina a duniya.

Sakamakon jin ra’ayin jama’a a kasar Amurka ya nuna cewa, yanzu haka dai Joe Biden yana gaba da Trump, kuma ya kara ba shi tazara a cikin kwanaki uku da suka gabata, bayan tabbatar da cewa cutar corona ta kama Trump, wanda a baya yake izgili da ita.

342/