ABNA24 : Shugaban kasar ta Syria wanda tashar talabijin din ‘The Fidza” ta yi hira da shi ya ce; “Yan ta’adda sun rika kwace yankuna daban-daban na kasar a karkashin taimakon kasashen Amurka , Faransa , Birtaniya, Qatar da kuma Saudiyya.
Shugaba Basshar Assad ya kara da cewa; Bayan bayyanar kungiyar ‘yan ta’adda ta Da’esh a 2014, da kuma taimako ta bayan fage da kasashen turai su ke yi musu, mun rika tattaunawa da kasar Rasha akan yanayi mai hatsari da aka shiga.
Shugaba Basshar Assad ya kuma yi ishara da yadda kasarsa da kuma Rasha suke fuskantar abokin gaba guda da shi ne; Ta’addanci.
Shugaba Basshar Assad ya kuma jinjinawa Rasha da Iran akan rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya.
342/