ABNA24 : Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu da akwai wasu mutane sama da talatin da suka jikkata a harin a cewar hukumomin yankin.
Harin dai an kai shi ne kan wani ginin gwamnati da ya kunshi wata barikin soji a lardin Ghani Khel, kamar yadda kakakin gwamnatin yankin ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.
Bayanai sun ce bayan tashin bam din maharan sun yi kokarin kusawa cikin ginin saidai dakarun dake wurin suka hallaka su.
Mafi yawan wadanda lamarin ya rusa dasu, jami’an tsaro ne, amma kuma akwai wasu fararen hula daga cikinsu.
Babu dai wata kungiya data dauki alhakin kai harin, saidai tuni hukumonin yankin suka danganta shi dana mayakan Taliban.
342/