1 Oktoba 2020 - 11:31
​Yemen: Sojojin Hayar Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula 2 A Lardin Al-Hudaidah

Sojojin hayar gwamnatin Saudiyya sun kashe mata biyu fararen hula hula a cikin lardin Al-daidah na kasar Yemen tare da jikkata wasu.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Almasirah ta bayar da rahoto daga birnin San’a fadar mulkin kasar Yemen cewa, a daren jiya mayakan haya na gwamnatin Saudiyay sun harba makaman atilare a kan kauyen Al-rabsa da ke cikin gundumar Hudaida, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mata biyu da kuma jikkatar wasu.

Wadannan hare-haren dai na zuwa kokarin da Saudiyya take yi tare da taimakon Amurka da wasu kasashen turai, domin mamaye lardin Al-hudaida mai matukar muhimamnci a kasar Yemen.

Ko a ranar Lahadin da ta gabata Saudiyya ta kashe fararen hula a cikin kauyukan Shajin, Al-Munqim da kuma Duraihami da ke cikin gundumar ta Al-hudaidai a yammacin kasar Yemen.

342/