28 Satumba 2020 - 11:06
Falastinawa Da Isra’ila Ke Tsare Da Su Na Shirin Fara Yajin Cin Abinci

Cibiyar da ke kula da lamurran fursunonin Falastinawa a gidjane kason Isra'ila ta sanar da cewa fursunonin za su fara yajin cin abinci.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran “ Palestine” ya bayar da rahoton cewa, sakamakon yadda Isra'ila take gallaza wa falastinawa da take tsare da su a cikin gidajen kaso saboda dalilai na siyasa, fursunonin za su fara yajin cin abinci a gidajen kaso biyar na Isra'ila.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin yahudawan Isra'ila take ta kara tsananta daukar matakai na takura wa falastinawa ne, inda wasu suna rasa rayukansu sakamakon rashin kula.

Baya ga haka kuma tana ci gaba da kame wasu falastinawan musamman masu nuna adawa da shirin yahudawa na mamaye wasu yankunan falastinawa.

342/