ABNA24 : Iran dai na zamarwa da Iraki makashin iskar gas da kuma wutar lantarki da ya kai kashi daya cikin uku da kasar Irakin ke bukata na wadatar da al’ummarta miliyan 40.
Bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ne, ta haramtawa kasashe ci gaba da mu’amula da Iran, ko kuma su gamu da fishinta.
Saidai tun lokacin ne take daga wa Iraki kafa, kafin ta samu sabbin abokan hulda.
A watan Mayu da ya gabata Amurka ta daga Irakin kafa har na tsawon watanni hudu domin ci gaba da sayan makamashin na iskar gas da wutar lantarki daga makobciyarta Iran.
Tattalin arzikin Iraki wacce gwamnatinta ke dasawa da Amurka da kuma Iran, ya fusknaci mummunan koma baya, sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, sai kuma matsalar annobar korona wacce ta kara dagula al’umma.
342/