ABNA24 : Gidan Rediyon faransa ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a Majalisar dinkin duniya ta bidiyo, Ramaphosa ya ce; a daidai lokacin da Majalisar ke bikin cika shekaru 75 da kafuwa, ya zama wajibi su kara jaddada bukatar ganin nahiyar Afirka ta samu wakilcin da ya dace a kwamitin tsaron, domin bayar da damar tattaunawa a mataki na koli a majalisar.
Ramaphosa ya ce ta hanyar sauya fasalin Majalisar ne kawai za a samu damar shawo kan wasu daga cikin dadaddun matsaloli da suka addabe ta.
Shugaban wanda ya ke jagorancin kungiyar kasashen Afirka ta AU, ya kuma bukaci dakatar da biyan basussukan da ake bin kasashen Afirka saboda illar da annobar korona ta yi musu, ganin yadda annobar ta hana gudanar da ayyukan ci gaba da dama, sakamakon yadda kasashen suka karkata kasafin kudadensu wajen tunkarar annobar, da sauran ayyukan kiwon lafiya.
Haka nan kuma Ramaphosa ya bukaci kara kaimi wajen yaki da cin hanci da rashawa wanda ya ce yana hana ruwa gudu wajen gudanar da lamurra da suka dace da kuma ingata rayuwar al’umma a kasashen nahiyar Afirka.
Tun kafin wannan lokacin dai kasashen Afirka sun jima suna fadi tashin ganin nahiyar ta samu wakilci a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, amma har yanzu ba su cimma burinsu ba.
342/