17 Satumba 2020 - 09:55
Venezuela Ta Yi Watsi Da Rahoton MDD Kan Take Hakkin Dan Adam

Gwamnatin Venezuela, ta yi watsi da rahoton MDD, dake zargin shugaban kasar Nicolas Maduro da wasu jami’an gwamnatinsa da yiwuwar hannunsu a take hakkin dan adam a kasar.

ABNA24 : Da yake sanar da hakan ministan harkokin wajen kasar ta Venezuela, Jorge Arreaza, ya ce rahoton shaci fadi ne kawai.

Ya ce rahoton shiri ne kawai na kiyayar da mahukuntan Washington ke nunawa kasar.

Ya kara da cewa babu kamshin gaskia a cikin rahoton wanda babu wata tawaga data sanya kafa a kasar domin gudanar da shi.

342/