15 Satumba 2020 - 12:12
Lebanon : An Samu Karin Jami’an Tsaro Da Suka Rasu A Rikicin Tarabulus

Shuwagabannin sojojin kasar Lebanon sun bada labarin cewa sun kara rasa ran wasu sojoji guda 4 a fafatawan da suke yi da ‘yan ta’adda a birnin Tripoli na areawacin kasar.

ABNA24 : Tashar talabijin ra Almayadeen ta kasar Lebanon ta ce majiyar sojojin ta bayyana cewa, sojojin sun sami nasar kashe Khalid Attalawi wanda ake nema saboda hannun da yake da shi a ta’asan da suka aikata a garin Kaftun.

Kafin haka dai sojoji 3 ne suka rasa rayukansu amma bayan mutuwar daya daga cikinsu wanda ya ji rauni, adadin ya karu zuwa 4 a halin yanzu.

Kafin haka dai Attalawi ya kashe wasu matasa guda 3 a yankin Kaftun kimani wata guda da ya gabata.

342/