ABNA24 : Kamfanin dillancin Labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Ra’isi yana fadar haka a jawabinda ya gabatar a wani taron yaki da miyagun kwayoyi a nan birnin Tehran a jiya Lahadi.
Alkalin alkalan ya ce, shan miyagun kwayoyi ya lalata iyalai da dama ya kuma zama babbar matsala ta zamantakewa, tattalin arziki da kuma al’adu a kasar ta Iran.
A wani bangare na jawabinsa Ra’isi ya ce, tallafin da kasar Iran take samu daga kungiyoyin kasa da kasa dangane da yaki da miyagon kwayoyi, bai fi na baka ba, da kuma bada lambobin yabo.
Daga karshe Ra’isi ya ce, kowa ya san cewa kasar Iran da gaske take a wajen yaki da miyagun kwayoyi a yankin kudancin Asisa.
342/