ABNA24 : “Yar sakon musamman ta wucin gadi ta MMD a kasar Libya, Stephanie Williams ce ta yi wannan gargadin tana mai kara da cewa; “Yan kasashen waje masu taimakawa bangarorin da suke fada da juna a kasar ta Libya, ba su aiki da takunkumin na hana shigar da makamai cikin kasar, wanda tun a 2011 aka shelanta shi.
Tare da cewa a yayin taron da aka yi a kasar Jamus dangane da kasar Libya a watan Janairu, da kuma kiran da kasashe da kungiyoyi 16 su ka yi na adaina shigar da makamai cikin kasar ta Libya, sai dai duk da haka ana ci gaba da keta shi.
Gwamnatin da take a birnin Tripoli tana samun taimako da goyon baya daga kasashen Turkiya, Qatar da Italiya, yayin da ‘yan tawayen da suke a gabashin kasar su ke samun goyon bayan Hadaddiyar Daular Larabawa, Faransa da Masar.
342/