24 Agusta 2020 - 14:53
Iraqi:Dakarun Hashdushaabi Sun Murkushe Hare-Haren Kungiyar Daesh A Lardin Ambar

Dakarun rundunar Hashdusha’abi ta mutanen kasar Iraqi sun sami nasarar murkushe hare-haren mayaka, ‘yan ta’adda na kungiyar Daesh a lardin Ambar na yammacin kasar a jiya Lahadi.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar dakarun ta na bada wannan labarin a jiya Lahadin.

Labarin ya kara da cewa bayan murkushe yunkurin ‘yan ta’addan, wasu daga cikinsu sun tsere, a yayinda wasu kuma suka fada hannun dakarun na Hashd.

Duk da cewa an kawo karshen ikon kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a arewa da kuma yammacin kasar Iraqi tun shekara ta 2017, amma har yanzun wasu ‘ya’yan kungiyar wadanda suke ta kai hare-hare a kasar nan da can, a duk fadin kasar, a duk lokacinda su ka sami damar yin hakan.

342/