ABNA24 : Rahotanni sun ce Amer Fakhuri ya mutu a jiya Litinin a wurin da yake zaune a kasar Amurka, bayan fama da rashin lafiya.
Tun a cikin watan Satumban 2019 ne dai jami’an tsaron kasar Lebanon suka cafke Amer Fakhuri a lokacin da ya iso birnin Beirut, inda aka tuhume shi da yi wa Isra’ila leken asiri a kasar a lokacin da Isra’ila tana mamaye da wasu yankuna a kudancin kasar Lebanon a shekaru 1980 zuwa 1990.
Fakhuri ya amsa cewa, ya yi wa Isra’ila aikin leken asir a cikin Lebanon, baya ga haka kuma yana daga cikin wadanda suka tsare tare da zabtar da dubban mutanen Lebanon a wasu gidajen kurkuku da Isra’ila ta gina a kudancin Lebanon a wancan lokacin, amma ya tsere bayan da Hizbullah ta fataki Isra’ila daga kasar ta Lebanon.
Haka nan kuma ya bayyana cewa, bayan da ya tsere daga Lebanon ya koma Isra’ila ne da zama baki daya, inda aka bas hi shedar zama dan kasa, daga nan kuma ya nufi Amurka, inda a can ma aka ba shi shedar zama dan kasa.
Kimanin watanni 5 kenan da kotun sojin kasar Lebanon bisa matsin lambar Amurka, ta bayar da umarnin sakinsa, bayan tsare shin a tsawon watanni 6 da nufin yanke masa hukunci, inda ya gudu zuwa ofishin jakadancin Amurka da ke Beirut, daga can kuma jiragen Amurka masu saukar anglu suka dauke shi zuwa Isra’ila, daga can kuma zuwa kasar Amurka, inda ya mutu a jiya bayan fama da wata rashin lafiya.
Jama’a da dama a kasar Lebanon dai sun yi farin ciki da jin labarin mutuwarsa, musamman ma wadanda ya kashe ko kuma ya azabtar da danginsu.
342/