ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Isma’il Baqayaa Homoneh jakadan kasar Iran a ofishin MDD da ke birnin Geneva yana fadar haka a yau Jumma’a a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron kwance damarar makamain nukliya a duniya.
Isma’il ya kara da cewa gwamnatin kasar Saudiya tana daga cikin kasashen da suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar NPT ta hana amfani da makamashin nukliya a matsayin makami, sannan HKI ce kadai ta mallaki makaman nukliya a yankin amma hukumar ta yi kamar ba ta gani bata ji a kan wadannan kasashe.
Daga karshen Isma’il ya kara da cewa faska biyu wanda hukumar IAEA take nunawa zai sanya shakku a cikin ayyukanta da adalcinta. Daga karshen ya bukaci hukumar ta gudanar da aikinta da ya zama wajibi a kanta a wadannan kasashe.
342/