12 Agusta 2020 - 10:03
Mali : An Sake Fitowa Zanga zangar Kin Jinin Shugaba Keita

A Mali, bangarorin dake zanga zangar neman shugaban kasar Ibrahim Bubakar Keita, ya yi murabus, sun sake fitowa a wannan Talata, a wani mataki na ci gaba da matsin lamba wa shugaban kasar.

ABNA24 : Zanga zangar na zuwa ne duk da kiraye kirayen kungiyar ECOWAS, ga bangarorin akan su magance sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa.

Rahotanni daga kasar sun ce dubban mutane suka halarci zanga zangar dauke da kwalayen dake dauke da rubutun ‘’ muna bukatar sauyi na gaske, IBK, ka kaice’’

Masu zanga zangar na kuma bukatar shi ma fira ministan kasar, Boubou Cissé, ya yi murabus.

Wasu bayanai na daban sun ce hatta ruwan saman da ake ta shashatawa basu hana masu zanga zangar fitowa ba.

Mai shiga tsakani na kungiyar ECOWAS, kana kuma tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana a wani taron manema labarai jiya a Bamako cewa har yanzu suna 342/kan lalubo bakin zaren matsalar kasar ta Mali.

342/