ABNA24 : Jalil Jalaifar wanda ya yi sanarwar ya kara da cewa zuwa cikin watan Satumba mai zuwa ne za a fara aiki da yarjejeniyar da aka cimmawa akan batun.
Jalaifar ya kara da cewa; tun tuni Iran tana fuskantar kalubale na jigilar amfanin gona zuwa kasar Rasha ta hanyar tekun Caspian, don haka bude sabuwar hanyar za ta warare wannan kalubalen domin za a yi amfani da Jiragen ruwa masu manyan nau’rorin sanyaya dakuna saboda kayan abinci.
342/