ABNA: Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a daidai lokacin da gwamnatin kasar Lebanon take fuskantar matsin lamba mai tsanani daga Amurka da kawayenta, domin ganin an kakkabe hannun Hizbullah a cikin dukkanin wani lamari da ya shafi tafiyar da gwamnatin kasar, a nata bangaren kotun duniya ta sanar da cewa a ranar 7 ga wanann wata na Agusta ne za ta fitar da hukuncinta na karshe kan kisan gillar da aka yi wa tsohon firayi ministan kasar Lebanon Rafiqul Hariri.
Tun bayan kisan Rafiqul Hari kusan shekaru 15 da suka gabata, kotun duniya ta fara bincike kan lamarin, inda aka bude wani reshe na kotun a cikin kasar Lebanon domin binciken wadanda ake tuhuma.
Manyan kasashen duniya musamman Amurka da kawayenta daga cikin kasashen turai masu tasiri Lebanon da kuma ‘yan korensu daga cikin kasashen larabawa, su ne suka yi ruwa suka yi tsaki a cikin dukkanin lamarin da ya shafi kisan Hariri da kuma batun hukuncin kotun duniya a kan hakan.
Isra’ila wadda ita ce a sahun farko da masana kan harkokin tsaro, da ma masu bin diddigin lamurran siyasar duniya da idon basira suke nuna yatsun tuhuma a kanta kan aikata hakan, saboda hanyar da aka bi wajen yi ma Hariri kisan gilla ya yi kama da irin nata, amma Isra'ila ba ta daga cikin wadanda ake tuhuma da aikata hakan daga bangaren kotun duniya.
Babban abin da ake zato dangane da hukuncin kotun shi ne, abin da Amurka da Isra’ila da kuma wasu kasashen turai gami da ‘yan amshin shatansu daga cikin kasashen larabawa suke bukata, wato a dora wannan zargi a kan kungiyar Hizbullah wadda ta tsone musu ido, kuma ta hana su cimma burinsu da bakaken manufofinsu a kan kasar ta Lebanon, wanda kuma ko shakka babu hakan zai yi tasiri wajen kara durmiyar da kasar cikin wani hali mawuyaci, wanda kuma saboda haka ne ake ganin cewa wannan shi ne dalilin da yasa ministan harkokin wajen kasar ta Lebanon ya yi murabus kwanaki biyu da suka gabata, saboda kusancin da yake da shi da Amurka da kuma kasashen turai musamman Faransa.
342/