4 Agusta 2020 - 12:09
​Najeriya: Rundunar Sojin Kasa Za Ta Yi Bincike Kan Harin Da Aka Kai Wa Zulum

<p "="">Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan harin da aka kai wa gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum.

ABNA: A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta bayyana cewa ba ta ji dadin abin da ya faru ba na kai wa tawagar gwamnan Borno hari ba, wanda ake sa ran mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kai shi.

Bayanin wanda kakakin rundunar sojin ta Najeriya Sagir Musa ya fitar, ya ce za a gudanar da kwakkwaran bincike a kan wannan hari da kuma gano yadda aka kai shi.

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnan na Borno ya yi zargin cewa sojoji ne da kansu suka kai masa hari a Baga, bisa zatonsu na cewa tawagarsa tawagar ‘yan Boko haram ce, ta yadda sojojin Najeriya ba su iya bambance tsakanin tawagar gwamna da ta tawagar ‘yan Boko Haram.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa, jami’an sojin Najeriya ba da gaske suke yi wa ba wajen yaki da kungiyar Boko Haram, inda ya ce lallai akwai wata manakisa a cikin lamarin.

342/